kungiyar kwalon dawaki ta Al amin ba zata kai labari ba

Shahararriyar kungiyar polo na kaduna al Amin na cigaba da shan kashi a gasar Dubai gold cup inda yazuwa yanzu an doke su a wasanni biyu da suka kara a can dubai duk kuma da yan wasan ta irin su Ibrahim Mohammed,Bello Buba da shi kansa uban tafiyar Mohammed Babangida.
A wasan al amin na farko a gasar, Dubai Falcons ta lashe ta daci 10-4 ranar alhamis sannan yau asabar Habtoor ta doke 11-1.Al amin zata buga wasanta na gaba da Ghantoot wacce ta barar wa Dubai Falcons da 9-10.
Ana saran kare gasar ranar jumma mai zuwa.

KIM CE TA LASHE GASAR AUSTRALIAN OPEN

Yar kasar Belgium me rike da kambin gasar US OPEN Kim Clijsters ta doke Li Na daga Sin 3-6, 6-3, 6-3 ta dauki kofin grand slam na hudu a tarihin ta.

MINISTAN WASANNI YA ZIYARCI KADUNA

Farfesa tauheed Adedoja,sabon ministan wasanni kuma shugaban hukumar wasanni ta kasa (NSC).Yace za’a baiwa jihar Kaduna muhimmanci tare da kulawa na musamman lokacin da gwabnatin tarayya ta soma gina kananan filayen wasanni a karkara a yunkurin ta na habbaka wasanni a matakin karkara.
Ministan ya bayyana hakan ne a karshen zirar gani da ido da ya kai fililayen wasanni dake Ahmadu Bello Kaduna ranar jumma’a.
Ya kuma yi alkawari inganta darajar dakunan kwanan yan wasa (hostel) domin maida shi otel kafin watan mayun wannan shekarar tare da umurni cewa a saka sunayen yan wasan da sukayi fice daga bangaren kassan a kofar dakuna otel bayan da aka kamala.
Farfesa Adedoja ya ziyarci filayen wasanni tanis,kwallon raga,kwallon bango,kwallon kafa da wajen ninkaya da dai sauran su.

MOURINHO NA TABABAN KASANCEWA A REAL-RAHOTANNI

Rahotanni dake fitowa daga spaniya na cewa kocin real madrid Jose Mourinho tababan cigaba da kasancewa a klub din real sakamakon fusatar dayayi na kin sayo karin dan wasan gaba da yake bukata don maye gurbin Gonzalo Higuain  da yasami rauni.
Ayayin da darectan wasanni Valdano da shugaban kungiyar real madrid and Florentino Perez sukafi son ya cigaba da baiwa Karim Benzema dama a maimakon sayo wani dan wasan gaba a kungiyar,tuni aka soma hasashe cewa yana tunanin ya koma tsohuwar kungiyarsa,InterMilan da yabarsu a watan Mayu ko kuma zai kuma Manchester City ko United. 

Shugaban NFF Maigari zai ziyarci Blatter


maigari
Aminu Maigari na kokarin bunkasa kwallon Najeriya
Shugaban hukumar kwallon kafa a Najeriya NFF Alhaji Aminu Maigari da Sakatare Janar Barrister Musa Amadu zasu ziyarci shalkwatar Fifa a watan Fabarairu.
Shugabanin NFF din zasu tattauna da shugaban Fifa Sepp Blatter da Sakatare Janar Jerome Valcke akan batutuwan da suka shafi bunkasa kwallon kafa a kasar.

Shugaban ofishin bunkasa kwallon kafa a Afrika ta yamma Mista Sampon Kablan wanda ya kawo zira a Najeriya ya ce kasar zata amfana matuka da wannan ziyarar ta shugabanin NFF zuwa Switzerland.
Mista Kablan yace"ina murnar gannin cewar akwai fahimtar juna tsakanin ma'aikatar wasanni da NFF, abune me kyau kuma zai kawo cigaba a fannin kwallon kafa".
Ziyarar bangariman da shugabannin NFF zau kai a shalkwatar Fifa a ranar uku ga watan Fabarairu na cikin tsarin da ake bi a duk lokacin da aka sauya shugabancin hukumar kwallon kafa a wata kasa a duniya.

MASU RIKE DA KOFIN SARKI NA SPANIYA NA DAKWON REAL KO ATHLETICO MADRID

Sakamakon nasarar da Sevilla ta samu na ci 3-0 kan villarreal ran talata,hakan ya bata cancantar shiga zagayen dab da karshe na gasar cin kofin Sarki a spaniya bayan ta hada kwallaye 6-3 a karshen wasanin da suka buga gida da waje.
Sevilla yanzu na jiran zakara a wasa tsakanin Athletico Madrid da Real wacce ta lashe sahun farko da kwallaye 3-1.Rabon madrid da daukar kofin dai tun 1993 a lokacin da ta doke Real Zaragoza 2-0 a wasan na karshe bayan ta kare a matsayi na biyu 1992 inda kishiyar ta Athletico ta mata ci 2-0.
Barcelona dai ita ta lashe kofin a2009 kuma ahalin yanzu tana kan hanya kaiwa semi final domin ita ke gaban Real Betis da kwallaye 5-0 a sahun farko. 

Aston Villa ta sayi Darren Bent Darren Bent

Darren Bent ne dan wasa mafi tsada da Aston Villa ta taba saya a tarihi

Aston Villa ta sayi dan wasan Sunderland Darren Bent a kan kudi fan miliyan 24, inda ya zamo dan wasa mafi tsada da ta siya a tarihi.

Tuni dan wasan mai shekaru 26 ya kammala gwajin lafiyarshi, inda ya kulla yarjejeniya da kulob din har zuwa shekara ta 2015.

"Kudaden sun fara ne a kan fan miliyan 18, zuwa miliyan 24," kamar yadda wakilin BBC Radio 5 Pat Murphy ya bayyana.

Ana saran dan wasan na Ingila zai fara taka leda a wasan da kungiyar za ta kara da Manchester City a filin wasa na Villa Park.

Wannan ciniki na Bent ya haura na fan miliyan 12n da Villa ta biya wajen sayen James Milner daga Newcastle a shekara ta 2008.

Shola Ameobi na murnar kiran da Najeriya tayi mashi


ameobi
Shola Ameobi
Dan kwallon Newcastle United Shola Ameobi ya ce yana murnar sake samun damar bugawa Najeriya kwallo a karon farko matakin Super Eagles.
Ameobi me shekaru 29, ya bugawa Ingila kwallo a matakin 'yan kasada shekaru 21 kuma an gayyaceshi ya buga a wasan sada zumunci tsakanin Najeriya da Guatemala a wata mai zuwa.
Haka zalika dan kwallon Wigan Athletic Victor Moses shima yana cikin wadanda aka gayyata a tawagar.
Kocin Super Eagles Samson Siasia ya ce Moses ya nuna farin cikin samun wannan damar amma dai kulob dinshi ya shaidawa BBC cewar bai sanarda ita ba akan gayyatar.
An haifi Ameobi ne a Zaria dake jihar Kaduna kafin ya koma Ingila tare da iyayenshi yana dan shekara biyar kuma shekaru goma da suka wuce an gayyaceshi ya bugawa Najeriya amma sai yaki yarda.